29 Disamba 2025 - 21:40
Source: ABNA24
Hamas Ta Fitar Da Bayani Bayan Shahadar "Abu Ubaydah"

Harkar Musulunci (Hamas) ta fitar da sanarwa a hukumance tana sanar da shahadar kwamanda Mujahidin "Hudhaifa Kahlut", wanda aka fi sani da "Abu Ubaydah", darektan kafofin watsa labarai na soja kuma kakakin rundunar Izziddin Qassam.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: A cikin wannan sanarwar, Hamas ta bayyana Abu Ubaydah a matsayin "murya Mai shiga rai" wanda ya kawar da barci daga idanun shugabannin mamaya kuma ya zamo mai zaburar da miliyoyin mutane 'yantattu kan hanyar 'yantar da Kudus da Masallacin Al-Aqsa.
Harkar Musulunci Ta Hamas ta sanar da cewa tare da zuciya mai cike da imani da alkawarin Allah da kuma alfahari da girmamawa, wannan kungiyar ta ke sanar da labarin shahadar kwamandan jarumai masu gwagwarmaya, "Huzaifa Kahlut" (Abu Ubaydah), kakakin jarumin rundunar Izziddin Qassam da aka shahadantar ga al'ummar Falasdinu, kasashen Larabawa da Musulunci, da kuma dukkan mutanen duniya masu 'yanci.

Sanarwar Hamas ta ce wannan babban kwamandan, wanda ya tsaya tsayin daka a kan abokan gaba kuma bai taɓa juya baya a fagen daga ba, ya sami babban matsayi na shahada bayan harin bam na matsorta da sojojin sahyoniya tare da iyalansa a ƙasar gwagwarmaya da jihadi Gaza. Abu Ubaidah ya sadaukar da rayuwarsa don manufar da ya kasance muryarta tsawon shekaru a cikin yaƙi mafi daraja a tarihin gwagwarmayar al'ummar Falasɗinawa, wato "Guguwar Al-Aqsa".

Your Comment

You are replying to: .
captcha